Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tankin Ruwa Ya Faɗo Ya Kashe Matashi A Potiskum

Daga Ibraheem Sabo  A ranar Lahadi 27/3/2021 al'ummar unguwar Ramin Ƙasa dake cikin garin Potiskum suka wayi gari da mummuna...Daga Ibraheem Sabo 

A ranar Lahadi 27/3/2021 al'ummar unguwar Ramin Ƙasa dake cikin garin Potiskum suka wayi gari da mummunan yanayi na faɗowar Tankin ruwa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wani matashi har Lahira. 

Wakilinmu ya yi tattaki har unguwar, inda ya tattauna da Mai Unguwar yankin, Malam Yusuf Idriss. Malam Yusuf ya bayyana yadda abin ya faru da cewa "muna fama da matsanancin rashin ruwa a wannan unguwa, shi ne sai ƙaramin ministan Ayyuka da Gidaje na ƙasa, Injiniya Abubakar D. Aliyu ya sa a tona mana 'Borehole' don muna samun ruwa. To wata biyu kenan da kammala aikin wannan 'Borehole' ɗin, sai kuma wannan iftila'i ya auku"

Mai unguwa ya ci gaba da cewa "yadda wannan al'amari ya faru kuwa shi ne, da dare misalin ƙarfe 2:10 na dare, sai shi wannan qaton Tankin da yake tara ruwan a sama, ya faɗo. To daman a jikin wannan gidan yake. Akwai ɗakin matasa da suke kwana a cikin gidan. To shi dai wannan Tankin a kan ɗakin matasan ya faɗo, ya danne su. Su huɗu ne a cikin ɗakin, ɗaya ya rasu daga cikinsu. Ɗaya kuma ya samu mummunan rauni, yanzu haka yana karɓar magani a Asibitin koyarwa, na Jami'ar jihar Yobe dake Damaturu. Sauran biyun kuma sun samu raunuka, amma ƙanana ne, har an sallamosu sun dawo gida"

"A lokacin da abin ya faru, na yi gaggawa na sanar da hukuma abin da yake faruwa, kuma da safe 'yan Sanda da jami'an tsaron farin kaya (DSS) sun zo sun yi rubuce-rubuce sun tafi. Shi matashin da ya rasa ran nasa sunansa Mohammed Musa, mai shekaru 27. Ibrahim Babagana shi ne yake karɓar magani a Asibiti, kuma kamfanin da suka yi aikin tona Borehole ɗin sune suke ɗaukar nauyin jinyar tasa. Sannan sun ce za su gyara dukkan abin da ya lalace sanadiyyar faɗowar Tankin" inji shi 

Sai dai al'ummar unguwar, suna ɗora alhakin faɗowar Tankin sakamakon rashin yin ingantaccen aiki. Wani a unguwar, da ya nemi mu sakaya sunansa, ya shaida wakilinmu cewa, "tun asali Kamfanin da ya yi aikin tona Borehole ɗin, basu yi shi da inganci ba. Ba a yi tono mai zurfi wanda zai riƙe turakun da za su ɗauki jibgegen Tankin da ruwan zai taru a ciki ba. Sai suka yi tonon ɗan kaɗan, bai shiga cikin ƙasa sosai ba, kuma hakan shi ne ya yi sanadiyyar faɗowar Tankin. Domin duk turakun sun fice daga cikin ƙasa"

Wakilinmu ya tattauna da mahaifin matashin da ya rasa ran nasa, inda yace "mu dai yanzu muna jira mu ji me gwamnati za ta ce a kai, tun da tana ta bincike kan lamarin. Ka ga wani ikon Allah, ba mu tashi daga zaman makokin ƙaninsa da ya rasu ba, sakamakon faɗawa ruwan kogi a garin Ngalda. Sai kuma ga wannan iftila'in shima. Tsakaninsu kwana shida. Kuma dukkansu 'ya'ya nane uwarsu ɗaya"

Ya zuwa haɗa wannan rahoton dai, hukumar 'yan Sanda tace tana bincike kan lamarin.

No comments