Wane Ne Sabon Ciroman Zazzau?

Daga Muhammad Farouk

Mai martaba Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli ya nada Alhaji Shehu Tijjani a matsayin sabon Ciroman Zazzau bayan cire Sai'du Mailafiya bisa zarginsa da rashin biyayya ga sabon Sarkin kamar yadda Jaridar MADOGARA ta labarto.

Alhaji Shehu Tijjani Alu Dan Sidi an daukaka darajarsa ne zuwa Ciroman Zazzau duba da biyayyarsa ga sabon Sarkin Zazzau Ahmed Nuhu Bamalli. 

Alhaji Shehu Tijjani a karkashin jagorancin sabon Sarkin an daukaka darajar sarautarsa sau biyu a cikin shekarar 2021 kawai. 

Da farko yana rike da sarautar Barden Kudun Zazzau, wanda mai Martaba Sarkin Zazzau Marigayi Alhaji Shehu Idris, CFR ya nada shi.  Kafin sabon Sarkin na Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli ya kara darajar sarautarsa zuwa Barden Zazzau sannan zuwa Ciroman Zazzau a yanzu. 

Sarautar Ciroman Zazzau dai dan sarki ake bai wa ita a masarautar Zazzau. 

Sabon Ciroman Zazzau din, Alhaji Shehu ya kasance Hakimin Kakuri Makera dake karamar Hukumar Kaduna ta Kudu. 

Sabon Ciroman Zazzau din ya fito ne daga gidan Mallawa. 

Post a Comment

0 Comments