Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Wata Kungiya Ta Nemi A Rika Tallafawa Wadanda Harin Ta’addanci Ya Tagayyara

  Daga Muhammad Farouk Wata kungiya mai suna ‘Initiative for Conciliation and Right Protection (ICRP)’ ta nemi da a rika tallafawa wada... Daga Muhammad Farouk

Wata kungiya mai suna ‘Initiative for Conciliation and Right Protection (ICRP)’ ta nemi da a rika tallafawa wadanda harin ta’addanci da na ‘yan bindiga ya tagayyara domin saukaka musu yadda za su gudanar da rayuwarsu.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a sanarwar da mataimakin Sakatare, jami’in hulda da jama’a da kuma Sakataren gudanarwa, Mable Bremah, Godwin Ekoja da Halima Bukar suka sanyawa hannu suka kuma rabawa ‘yan jarida a ranar Asabar.

Sanarwar ta ce wadanda hare-haren ta’addanci da kuma na ‘yan bindiga ya shafa da kuma wadanda ake zalunta sun cancanci kulawa ta musamman wanda hakan zai taimakawa wadanda abin ya shafa su fara dawowa hayyacinsu.

Har wala yau sanarwar ta nemi ‘yan Nijeriya da su hada hannu wuri guda ba tare da nuna bambancin addini, kabila, ko siyasa ba wajen kawo karshen matsalar tsaro da yake addabar kasarnan.

Sanarwar ta ce ‘yan Nijeriya na rayuwa ne yanzu a wani mawuyacin hali, inda mutane rayuwarsu ya zama kamar ba a bakin komai ba. Kungiyar ta ci gaba da cewa; kasarnan na fuskantar habbakar cin hanci da rashawa, ta’addanci da kuma zalunci, inda suka ce lamarin na ci gaba da kazanta a kowacce rana.

 “rayuka na salwanta da yawan gaske, fata da mafarkin mutane na karewa. Hakan na sanya mutane cikin halin kunci, damuwa da kuma shiga halin ni ‘ya su”, suka lurantar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “da farko wata kungiya ce da ake kira da ‘Boko Haram’, wadanda ake cewa sun tsani karatun Boko. Daga baya kuma, bayan bayyana su a matsayin kungiyar ta’addanci, sai suka rika kai wa wuraren ibada, kasuwanni da kuma tarukan wadanda ba su ji ba ba su gani ba hare-hare, lamarin da ya sanya masu tunani tantama”, suka lurantar.

Kungiyar ta ce wadannan hare-hare ya shafi ‘yan Nijeriya da dama, ko dai kai tsaye ko akasin hakan. “lamarin za a iya cewa ya fi shafar arewa maso gabashin Nijeriya, amma hare-haren ya shafi a tsawon shekarun nan ya shafi kungiyoyi addini da kabila daban-daban”, inji su.

Sanarwar ta nusasshe da cewa; ba kwai cibiyoyin ilimi aka rika kai wa hari ba, hatta kasuwanni, wuraren da jama’a ke taruwa, an rika kai wa hari, lamarin da ya sanya kungiyar suka ce dole a sanya alamar tambaya akan abin da aka ce ‘Boko Haram’ sun tsana.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “wuraren ibada kamar coci, masallatai, da kuma tattakin da ‘yan shi’a ke yi duk an kai musu hare-haren boma-bomai. Wannan ya nuna cewa hare-haren ya ma fi shafar musulmi fiye da kiristoci”, ya lurantar.

Kungiyar ta ce duk da ana alakanta kungiyar ta’addancin da ‘musulunci’, amma me yasa suka fi kai wa musulmi hari? Suka tambaya. Wanda suka ce lamarin ya zarce abin da ido ke gani kawai.

Sanarwar ta ci gaba da cewa; daga bisani ne kuma sai wadansu ‘yan ta’addan da sunan ‘yan bindiga da masu garkuwa da jama’a suka bulla, wanda hakan ya kara jefa kasar cikin zullumi.

“wannan ya sanya shakku ganin cewa jihar Zamfara da suka fi fuskantar hare-haren ‘yan bindiga suna da arzikin gwala-gwalai da zinare da sauran arzikin kasa, shin hare-haren ba shi da alaka da arzikin jihar kuwa?” suka tambaya.

Kungiyar dai ta ce ta yi imanin cewa wannan wani sabon makirci ne na sanya jihar cikin tashin hankali da tarwatsa al’umma wanda hakan zai bai wa wadanda suke daukar nauyin ‘yan bindigar su samu damar ci gaba da kwashe tattalin arzikin jihar.

Kungiyar ta yi tilawar cewa abin bakin ciki ne da ya zama ba kawai ‘yan ta’adda ne ke kashe fararen hula ba a Nijeriya, inda ta zargi yadda wadansu jami’an tsaron kasar wanda ya hada da ‘yan sanda da sojoji da kai hare-harekan fararen hula suna kashe su.

Kungiyar ta yi tilawar yadda jami’an soja da na ‘yan sanda a lokuta da dama suka rika kai hare-hare kan jerin gwanon na lumana na fararen hula a kasar wanda suke kalubalantar matsalolin da yake addabar kasar.

“misali shi ne kisan kiyashin da sojoji suka yi a 2015 inda suka kashe dubban fararen hula da yi bizne su a ramin bai daya domin bizne ta’addancin da suka aikata. Ba ya ga hakan, daruruwa da dama sun bace ba a san inda suke ba, sannan kuma jagoran ‘yan shi’a da matarsa har yanzu ana ci gaba da tsare su duk da umurnin da kotu ta bayar a cikin watan Disambar 2016 cewa a sake su”, suka lurantar.

Har wala yau a cikin sanarwar da kungiyar ICRP ta fitar din, ta ce harin da aka kai wa masu zanga-zangar #ENDSARS a Lekki, shima wata shaida ce da ke nuni da yadda sojoji ke take hakkin ‘yan Nijeriya.

“abin takaici, zanga-zangar #ENDSARS da aka shirya domin kawo karshen take hakkin bil’adama da ‘yan sanda ke yi a Nijeriya sai ya zama jami’an tsaron Nijeriya sun dira kan masu zanga-zangar lumanar da aka fara tun kafin ma wadansu bata gari su kutsa cikin masu zanga-zangar domin kawu rudani”, inji su.

Kungiyar ta ce haka zalika, za a iya tuna yadda ‘yan sanda a lokuta da dama suka rika kai hare-hare kan mabiya mazhabar shi’a a Abuja a lokutan muzaharorinsu, inda suka ce abin takaici ne na yadda mutane ba sa damuwa da irin lamuran nan.

Kungiyar ta ce hare-haren yanzu ya bayyana kamar hasken rana na yadda ake dira kan jaruman da ke fadin gaskiya suke kuma kalubalantar zalunci.

 

ICRP ta ce ba ya ga gallazawa ‘yan kasa da ake yi, ana kuma tafka cin hanci da rashawa, garkame mutane ba bisa ka’ida ba, mallake kayayyakin al’umma, kisan wadanda ba su ji ba ba su gani ba akan tituna.

 “raunana ‘yan Nijeriya har yanzu ana kai musu hare-hare tare da danne su da kaga musu sharri, a yayin da masu aikata wadannan abubuwa ke ci gaba da tsanantawa. Dukkan wani mai ‘yan adamtaka ba zai yi shiru bisa irin wadannan abubuwa da suke faruwa”, suka jaddada.

Kungiyar ta ICRP ta yi nuni da yadda a zamanin nan wadanda suke aikata zalunci suke yawo abin su gaba-gadi, amma wadanda ake zalunta musamman masu fadin gaskiya da yaki da zalunci da danniya ake ci gaba da danne su da kuma garkame su ba bisa ka’ida da adalci ba. Tare da danne musu hakkinsu na rayuwa cikin ‘yanci, inda suka ce sun ga abin da ya faru da Dadiyata. Inda suka ce lallai wannan gwagwarmayar abin a yi ta ne domin  ‘yantar da wannan al’umma.

Kungiyar ta ICRP ta nuna takaicinta na yadda shirun da al’umma ta yi ke kara karfafar masu aikata zaluncin a kasar, inda suka ce rashin masu gwagwarmayar da za su kalubalanci masu zalunci ne ke kara jefa kasar cikin bala’i. “a matsayinmu na mutane, dukkaninmu al’umma daya ce, ka da ku jinkirta ba da gudummawarku a wannan fafutika. A don haka mu yi watsi da son ranmu, mu hadu wuri guda wajen daga muryoyinmu”, inji su.

Sun karkare da cewa; kowanne dan kasa akwai gudummawar da zai bayar wajen ci gaban kasarnan ta Nijeriya. Inda suka ce; dukkaninmu wanda ya hada fararen hula, sojoji, ‘yan sanda, ‘yan siyasa, akwai gudummawar da za su bayar wajen dawo da zaman lafiya mai dorewa da kuma ci gaba Nijeriya. “dukkanin wadanda hare-haren ta’addanci ya shafa suna cikin halin ni ‘ya su a yanzu a Borno, Katsina, Zamfara, Neja, Kaduna da kuma wadanda aka zalunta kama ga masu zanga-zangar ENDSARS da kuma ‘yan shi’a, da al’umma Binuwe da na gabashin kasarnan”, suka tabbatar. 

No comments