Yadda Rashin Lafiya Ya Yi Sanadin Rayuwar Direban Shugaba Buhari A Abuja


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika sakon ta’aziyya ga iyalan Afaka bisa rasuwar direbansa, Sa’idu Afaka wanda ya mutu a asibitin fadar a ranar Talata bayan doguwar rashin lafiya a daidai lokacin da shugaban kasar ke neman ta shi lafiyar a asibiti a birnin Landan.

Shugaba Buhari ya jajantawa gwamnati da jama'ar Jihar Kaduna, inda ya bayyana Marigayi Afaka a matsayin mutum mai gaskiya, iya aiki da rikon amana wanda ya tafiyar da aikinsa cikin matukar kulawa.

Shugaban ya tuna a shekarar 2016, yayin da yake aikin hajji a Saudiyya, marigayin wanda soja ne ya tsinci wata jaka da makudan kudaden kasashen waje ya mika ta ga Hukumar aikin hajji ta kasa, matakin da ya jawo masa yabo daga hukumomin Saudiyya da na Nijeriya.

Daga karshe ya kara da rokon Allah ya bai wa Iyalansa da abokansa hakurin jure wannan rashin.

Post a Comment

0 Comments