Yadda ‘Yan Bindiga Cikin Shigar Mata Suka Kai Mummunan Hari A Garin Zariya

Al'umma sun yi cirko-cirko a Unguwar da lamarin ya auku. 

-Sun yi awon gaba da matan aure biyu

-An cafke mutum biyu a cikin ‘yan bindigar

-Sun jikkata mutum hudu

Daga Ammar Muhammad, Muhammad Badamasi

A daren jiya Lahadi 25 ga watan Afrilun 2021, wadansu ‘yan bindiga suka kai hari a Unguwar Lowcost dake cikin garin Zariya a jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da matan aure biyu tare da jikkata matasa guda hudu. Sai dai kuma ‘yan banga sun yi nasarar cafke mnutum hudu daga cikin masu garkuwa da jama’ar kamar yadda ganau suka tabbatawa da MADOGARA

Wakilanmu a Zariya da safiyar yau Litinin 26 ga watan Afrilun 2021 sun kai ziyara zuwa ga Unguwar domin bin bahasin abubuwan da suka wakana, inda suka tarar da cincirindon al’umma da dama a lungu da sako-sako na unguwar cikin yanayi na jimami da alhinin abin da ya faru. 

YADDA ‘YAN BINDIGAR SUKA KAI HARIN 

A yayin da 'yan jarida ke hira da Ibrahim

Ibrahim Muhammad Sani, daya daga cikin wadanda harin ‘yan bindigar ya rutsa wanda yake zaune a gidan Yayansa  Haruna Muhammad Sani da aka yi garkuwa da matarsa, ya shaidawa wakilinmu yadda lamarin ya auku, inda yake cewa; “a jiya da daddare wajen karfe 10, kowa na cikin gida, ni kuma ina zaune haka muna zaune. Ni kuma dama na kan fita na dawo karfe goma, ko da na dawo na kulle gida. ‘gate’ guda biyu ne dama a gidan namu, na shigo ta ‘gate’ din farko da na saba shiga, na sanya babur dina na kulle gidan sannan na tafi daki. Na shiga daki na zauna a kujera sai kawai na ce bari na sanya wayata a caji na yi alwala na yi sallah. Ko da na shiga bayi ina alwala, na zo ina wanke hannun hagu sai na ji daram-dam-dam sau hudu a jere. Sai na yi tunanin ko ‘yan banga ne da suke buga bindiga, sai kuma na ga ashe lokacinsu bai yi ba, karfe sha biyu suke buga na su (kuma lokacin sha biyu bai yi ba)”, inji shi.  

Ibrahim na amsa tambayoyin wakilinmu

Ibrahim ya ci gaba da cewa; “sai kawai na fito domin na tabbatar ko janareto dinmu ne, sai kuma na ga wutarmu ba ta samu matsala ba. Ko da zan fito kawai sai muka yi karo da guda daya wanda suka shigo tsakar gidan. Ko da muka yi karo na juya zan gudu, sai yana ce min ‘zo nan, zo nan’, na gudu a guje na shanye kwana. Sai ya yanko ya yi harbi bai same ni ba. Sai na samu na tsira na shiga cikin daya daga cikin dakin dake gidan. Sai suka shiga wani daki suna nema na, amma ba su ganni ba,” ya tabbatar mana. 


Ya kara mana da cewa; “sai daga baya komai ya lafa muka sake fitowa zamu duba mu ga daya dakin Uwargidan domin mu ga halin da take ciki. Sai muka kara jin wani daki daban an kara harba bindiga tai kara, sai muka kara komawa. Can sai muka ji usur din ‘yan sanda, sai muka fito, muna fitowa, ko da muka je dakin Uwargidan muka duba mu ka ga falonta wayam, sai muka bubbuga dakin maigidan saboda dakin na da kofar da take shiga falonsa ta nan, sai muka bubbuga muka ce yaran su bude, suna budewa muka ce mune, sai muka ce musu ina mamanku? Sai suka ce sun barta a falo. Da yake akwai namiji dan karami dan shekara tara, ya ta sa su suka shige dakin suka shige ‘wardrop’ dinshi na kaya, muka ce musu; ina mamansu? Suka ce ai ba su ganta ba, daga nan ne aka lura ashe sun tafi da mamar”, ya tabbatar.

Ibrahim ya bayyana yadda ‘yan bindigar suka tafi da matan auren guda biyu, daya a gidansu daya kuma daga makwabtansu, inda yake cewa; “wanda suka tafi da ita sunanta Fulera, a gidanmu ita kadai suka tafi da ita. Sai kuma matar makwabtanmu da ake ce masa Oga Bala ma’aikacin kwastan ne, ita ma Hajiyar sun tafi da ita da ‘ya’yanta guda biyu mace da namiji wato Maryam da Halifa da ‘yar aikin, sai daga baya da safe aka ga ‘yar aikin da yaran guda biyu sun sake su. Yanzu dai sun tafi da mata biyu (da matar gidanmu da na makwabtanmu)”. 

Gidan Oga Bala da 'yan bindigar suka kai wa hari suka tafi da matarsa, Hajiya Mariya. 

Fulera mai shekara kusan 50, wanda take ‘yar aiki ce a gidan Mariya Bala (wacce ita ma aka yi garkuwa da ita), ta shaidawa wakilinmu yadda ‘yan bindigar suka shiga gidansu, inda take cewa; “mu muna cikin daki muna zaune, sai yara suka zo suka ce mana ga barayi nan, muna zaune sai muka ce innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, muna ta tsuma, sai suka shigo suka yi can suka sake dawowa suna ta dukan kofarnan, muna dannowa harda yaran, suna ta dukan kofarnan, har sai da suka banbare kofar, suna buge kofar, suka fito suka kada mu kofar gida. Da suka kada mu kofar gidan nan sai suka kore mu da ni da yaran, ita kuma sai suka yi can haka da ita (suka tafi da ita),” ta tabbatar. 

Malama Fulera da ta tsira bayan 'yan bindigar sun sake ta tana hira da wakilanmu. 

Fulera ta ce; “mu hudu suka kama, daga mu sai yaran. Amma daga karshe sai suka kore mu da ni da yaran, ita kuma sai suka tafi da ita. Sunanta Hajiya Mariya. ‘yan bindiga biyu suka shigo mana nan gidan, daya da Nikab, daya ba nikab. Mara nikab din ne mai dukan kyauren, dayan kuma ya yi can hakan yana haske-haske. Wanda kuma ya sanya mu muka fita kofar gida akwai bindiga a hannunsa. Shigan mata suka yi sosai,” ta tabbatar.

Shima daya daga cikin maigidan da aka tafi da matarsa wato Haruna Muhammad Sani ya labarta mana yadda ya samu labarin kai harin a gidansa, inda yake cewa; “lokacin da na samu labari na zo ne ina cikin Lowcost, ina gab da gidana kawai sai na ga waya. Da na ga wayar ba suna da kamar ba zan daga ba, kawai sai na dauka dai, sai na ji kanina ne ya ce min gidan nan ba lafiya, masu garkuwa da jama’a na ciki, na yi maza na juya”. 

Haruna Muhammad, maigida ga Fulera Haruna da aka yi garkuwa da ita na ganawa da wakilanmu. 

Haruna ya ci gaba da cewa; “ko da zan juya sai ake ba ni labarin lallai suna nan sun dirar wa matata, sun zagaye min ‘gate’, sun bude kofar falo sun shiga, ko da suka shiga sai suka tasa ta akan ina nake? Ta ce bana nan, shi ne suka ce mata ta wuce su tafi. Yaran da suka tashi kuma sai suka samu wuri suka boye”.  
 
YADDA BABBAR YARINYAR MAIGIDAN TA SHA DA KYAR A HANNUN ‘YAN BINDIGAR 

Ibrahim Muhammad Sani har wala yau ya bayyana mana yadda babbar yarinyar maigidan ta sha da kyar daga hannun ‘yan bindigar, inda yake cewa; “ita kuma akwai babbar yarinyar gidan, a lokacin tana ‘kitchen’ tana soya wa maman kwai, jin haka kawai sai ta fita a guje, sai suka bi ta a guje suna harbinta, ba su same ta ba, ta samu ta shige wani gidan tana ihu cewa masu garkuwa da jama’a sun zo gidanmu, sai suka harbi yara uku a unguwar namu. Daya a hannu aka harbe shi, daya a gefen ciki, dayan ma a hannu”, ya tabbatar. 

Cikin gidan Haruna Muhammad da aka sace matarsa. 

Shima mahaifin Mufeedah, Haruna Muhammad Sani ya tabbatar mana da yadda ‘yar ta shi ta sha da kyar a hannun ‘yan bindigar, inda ya shaida mana cewa; “ita babbar ‘yata (Mufeedah) da suka same ta a ‘kitchen’ tana soya kwai, sai suka tasa ta a gaba, ko da za ta bi hanya ta gudu, sai suka fara harbi shi ne garin harbin ba su same ta ba, sai suka sami yara guda hudu a nan makwabtanmu, yanzu haka suna nan a asibiti”, ya tabbatar. 


WADANDA AKA HARBA SUNA ASIBITIN NEW CITY DAKE LOWCOST 

Ibrahim Muhammad Sani ya tabbatar mana da cewa; wadanda aka harba mutum hudun suna asibitin New City dake nan Unguwar ta Lowcost suna karbar magani. 

Uku daga cikin hudu da aka harba a Asibitin New City

Haka zalika ko da wakilinmu ya isa asibitin ya tarar da jama’a makare a bakin shiga asibitin, amma ya yi nasarar ganawa da wadanda aka jikkata, inda ya tarar da har an yi musu magani, kuma raunin na su da sauki. 

Cikon na hudun da aka jikkata a harin.

JAMI’AN TSARO BA SU BADA DAUKI DA WURI BA

Ibrahim Muhammad Sani ya nuna takaicinsa na yadda jami’an tsaron ‘yan sanda ba su bayar da dauki yadda ya kamata ba, wanda ya ce da sun yi abin da ya kamata da lamarin bai kazanta haka ba, inda yake cewa; “wadanda na gani wanda suka shigo cikin gidanmu sun kai su shida. A gidanmu sun kwashe akalla minti arba’in. A Unguwarnan sai da suka yi awa biyu gyam, amma a ce a tsawon awa biyu an rasa wanda zai kawo dauki? Da a ce a lokacin da suka fara abin aka kawo dauki, za a cin musu saboda sai da suka shiga gidanmu suka dade, sannan suka shiga makwabtanmu. Sannan suka gudu suka kara zuwa suka kai wa wadansu gidajen farmaki amma duk ba a samu dauki ba sai na ‘yan banga wanda su suka rika binsu da makamai suna gangarawa ramuka da lunguna suna dubawa irin ginin da ba a karashe ba ko za su gansu. A haka dai suka gudu”, ya tabbatar. 

Ya kara da cewa; “a lokacin mun samu daukin ‘yan banga. ‘Yan sandan an je an yi musu korafi, amma sai suka ce sai DPO ya zo, suna ta rabe-rabe, ‘yan banga ne kawai da taimakonsu da taimakon Allah suka shige gaba. Ko da suka zo, dan sanda daya ne ya zo da bindiga shi kadai. Ko da ‘yan sandan suka zo layin sai suka koma jikin garu suka manne. ‘Yan bangan ne suka yi artabu da guda daya ya samu ya tsere, sai a can wajen sabuwar unguwa ana ce mata Buzai da take Lowcost din, aka yi nasarar cafke guda biyu” ya tabbatar. 

Daya daga cikin gidajen da 'yan bindigar suka shiga. 

Sai dai kuma maigidan da aka yi awon gaba da matarsa Fulera Haruna, ya yi mana karin haske dangane da zuwan jami’an tsaron ‘yan sandan, inda ya bayyana mana cewa; “bayan na juya na je ofishin ‘yan sanda na Lowcost na shaida musu. Kasa da minti goma sai ga su, da suka zo da motar Hilux sai na ce musu ai suna nan a cikin gidana fa, mu gangara da motar, sai suka nuna a’a, bari su tsaya mu gangara kasa, ko da mu ka gangara kasa sai masu garkuwa da jama’ar suna harbi, suma ‘yan sandan na harbi. ‘Yan sandan sun zo a mota kirar Hilux biyu, sun yi kokari sosai, domin sun zo kamar su goma akalla. Sai kuma ‘yan banga da yardar Allah suma sun yi kokari sosan gaske. Sune ma suka kama biyu daga cikin masu garkuwa da jama’ar suka damka su ga ‘yan sanda”, ya tabbatar. 

‘YAN BINDIGAR SUN FARFASA WA JAMA’A GARU

Yadda suka fasa kofar shiga dakin daya daga cikin gidajen da suka shiga. 

Wakilinmu ya lura da yadda ‘yan bindigar suka farfasa wa mutanen unguwar garunsu da harsasai. Inda ya kirga gidaje guda shida da harsasai ya huda su. 

Kuna iya kallon hujin harsashi a cikin bangon. 

“sun harbi garun gidanmu. Ga fitar harsasai nan. Tun daren an haska an tsinci harsasai guda talatin wadanda suka harba. Sun harbi ‘gate’ din wani makwabcinmu mai kallon gidanmu har ma ya fasa tayan motarsa”, inji Ibrahim.  

Sun yi wa kofar gidan nan harsasai. 

Yadda suka fasa daya daga cikin garun gidajen da harsasai. 

HAR YANZU ‘YAN BINDIGAR BA SU TUNTUBI IYALIN WADANDA SUKA SACE BA

Dangane da ko ya zuwa hada rahoton nan ‘yan bindigar sun kai ga tuntubarsu, Ibrahim ya kada baki ya ce; “har yanzu ba su kai ga kiran waya ba. Wayar dai matan gidan namu muna kira tun ba a dauka, suka dawo suna danna ‘busy’, yanzu kuma wayar ma a kashe”, ya tabbatar. 

Shima maigidan na ta, Haruna Muhammad Sani ya bayyana mana cewa; “ya zuwa yanzu babu wani labari daga gare su. Domin ko a jiyan kafin su fita unguwar na rika kiran wayarta sai suna yanke mata wayan. To ashe sun shiga makwabtanmu ma ban sani ba suna kokarin tafiya da dayar matan da ‘ya’yanta. Ba su dauki ‘ya’yana ko daya ba, mata ta kawai suka tafi da ita”, ya tabbatar. 

‘WADANDA SUKA KAWO MANA HARI FULANI NE’

Mutum biyun da aka kama cikin 'yan bindigar

Haruna Muhammad Sani ya yi zargin cewa wadanda suka kai musu hari a Unguwar Fulani ne, sai dai ya ce akwai wanda ma ba musulmi bane a cikinsu cikin wadanda aka kama, inda yake cewa; “an yi nasarar kama guda biyu daga ciki. Daga baya ‘yan banga sun zo, su kuma ‘yan bindigar sun yi yunkurin su fita ta can, sai suka gansu, shi ne sai suka kama su. Yanzu haka suna ofishin ‘yan sanda suna bincikensu,” ya lurantar.

Ya ci gaba da cewa; “wadanda suka kawo mana hari Fulani ne. Amma dayan da aka kama yanzu ba ma musulmi bane. Amma dayan bafullatani ne”. 

Dangane da yawan ‘yan bindigar da suka kawo musu hari kuwa, ya kada baki ya ce; “wasu sun ce sun kai akalla talatin, amma ni dai ban gan su ba. Amma lallai suna da yawa. Da suka shigo unguwar sun karkasu ne”, ya tabbatar. 

Post a Comment

0 Comments