Yadda 'Yan Bindiga Suka Fasa Gidan Yari Da Kai Farmaki Hedikwatar 'Yan Sanda A Jihar Imo


Wasu mahara dauke da bindigogi da ababen fashewa sun fasa babban gidan yari da Hedikwatar 'yan sandan jihar Owerri, inda suka saki daruruwan wadanda ke tsare.


Rahotanni daga jihar Imo da ke kudancin Nijeriya na cewa wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki a gidan yarin Owerri​ babban birnin jihar, inda suka saki fursunoni fiye da 1500 da safiyar yau Litinin.

Wata majiya ta ce ‘yan bindigar sun kai farmakin ne tsakanin karfe 1 zuwa 4 na safiyar yau Litinin.

Haka kuma maharan sun cinnawa shelkwatar rundunar ‘yan sandan jihar wuta a Owerri​, inda suka kona kusan dukkan motocin da ke harabar.

Bugu da kari ‘yan bindigar sun balle tare da sakin dukkan wadanda ake tuhuma da ke ajiye a sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan.

An jiyo maharan suna cewa fursunonin su fice zuwa gidajensu, bayan da suka fasa ginin gidan yarin da wata nakiya da wasu abubuwan fashewa.

Wasu majiyoyi da ke da alaka da hukumar tsaro, sun fadawa jaridar Daily Times cewa, maharan da suke dauke da makamai, sun rera wakokin gwagwarmaya a sha tale-talen fadar gwamnatin jihar, kafin su aukawa wuraren.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Imo ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta bakin kakakinta Orlando Ikeokwu, duk da yake ba ta ba da cikakken bayani akan harin ba ya zuwa lokacin hada wannan rahoton kamar yadda gidan Rediyon Amurka ya tabbatar. 

Post a Comment

0 Comments