'Yan Bindiga Sun Addabi Kauyukan Zariya


Daga Wakilinmu

A 'yan kwanakin gabanin shigowar azumi da cikin watan Ramadana bayanai sun tabbatarwa da MADOGARA cewa; wadansu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun adddabi kauyukan Zakara, 'Yan Durma, Mangi, Siddi da sauran kauyukan dake kewaye da garin Zariya ta jihar Kaduna.  

Bayanan wanda muka samu daga ganau sun tabbatar mana da cewa 'yan bindigar na zuwa ne akan babura da muggan makamai inda suke awon gaba da mutane da dabbobinsu tare da yi wa rayuwarsu barazana. 

Al'umma da dama da suke zaune a Kauyukan sun shaida mana cewa suna cikin firgici da su da dukiyoyinsu, inda yanzu ba sa bacci da ido biyu. Tuni da dama suka yi kaura suka bar kauyukan suka dawo kwaryar Zariya. 

Bincikenmu ya nuna cewa kauyukan ba su samun wani dauki daga jami'an tsaro a yayin da 'yan bindigar ke farmakar kauyukan. 

Duk wani kokari da muka yi domin jin ta bakin hukumomin tsaro a garin na Zariya, lamarin ya ci tura ya zuwa hada rahoton nan.

Post a Comment

0 Comments