‘Yan Bindiga Sun Farmaki Sojin Nijeriya, Sun Yi Awon Gaba Da Makamai Da Miliyan 28


Daga Muhammad Farouk 

Wadansu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da naira miliyan ashirin da takwas bayan da suka kai wa wadansu ba’adin rundunar sojin Nijeriya harin kwantan bauna wadanda aka aika domin bada karfi a jihar Binuwe. 

Rundunar sojin Nijeriya suna kan hanyarsu ta zuwa jihar Binuwe domin sasanta rikicin kabilanci da yake aukuwa a jihar ta Binuwe kamar yadda majiyarmu ta soji ta tabbatar. 

Majiyarmu ta shaida mana cewa; sojojin sun taso ne daga karamar hukumar Katsina-Ala domin kai makamai zuwa karamar hukumar Oju wanda yake kilomita 171 daga Katsina-Ala, inda ‘yan bindigar wadanda ake zargin sun fito ne daga yankin Konshisha a jihar ta Binuwe suka fi karfin sojin a harin da ake kyautata zaton sun kai musu a ranar Talata. 

Wani babban jami’in soja wanda yake tare da rundunar sojin a lokacin da lamarin ya auku, ya ce harin kwanton baunar wanda ‘yan bindigar suka kai, sun bace nan take bayan sun kammala kaddamar da harin, inda suka bi dare ta kogin Binuwe suka gudu. 

 “tabbas ‘yan bindigar sun saci makamai da kudaden da ya kai naira miliyan 28 daga hannun sojojin”, inji babban jami’in sojan. “yanzu haka an kaddamar da bincike kan lamarin tunda hedikwata suka samu labarin”, ya tabbatar. 

Babban jami’in sojan ya ce ba a zargi kowanne soja ba kan afkuwar lamarin, “amma tabbas abin damuwa ne”, duba da yadda ‘yan bindiga har za su iya samun wannan dama ta kai harin nan. Sai dai har yanzu majiyarmu ba ta yi mana cikakken bayani ko ta ya ya aka samu wadannan zunzurutun kudi a hannun sojoji haka ba. 

Babban Kaftin din soja, A.T. Adedayo da ya jagoranci tawagar rundunar sojin har ya zuwa yanzu ba a san inda yake ba, da kuma wani babban makami na bindiga da harsasai fiye da dubu biyu. 
Wata majiyarmu ta ce ba a tarar da komai ba a inda aka kai wa sojojin hari a yayin da aka sake tura wata tawaga ta je ta duba inda aka kai harin a Oju. 

Wani hadin guiwa ta runduna ta 72 da Bataliya ta musamman da kuma jami’an dakile garkuwa da jama’a da kuma Operation Whirl Stroke (OPWS), tuni suka kaddamar da bincike domin ‘yanto sojojin da suka bace kamar yadda majiyarmu ta tabbatar mana. 

Kakakin rundunar sojin Nijeriya bai samu tofa albarkacin bakinsa ba kan lamarin, domin majiyarmu ba ta same shi ba har ya zuwa hada rahoton nan.

Post a Comment

0 Comments