'Yan Bindiga Sun Kai Hari A Abuja,


Yan bindiga sun mamaye wani yanki na Fulani inda suka harbe wani dan shekara 30 Abdulmumin Jagaba kusa da kauyen Sabongari a yankin Kwali da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Wani mazaunin yankin ya ce lamarin ya faru ne da karfe 11 na daren ranar Litinin lokacin da yan bindigar suka yi wa yankin zobe tare da bude wa mamacin wuta.

Ya ce yan bindigar sun harbi Jagaba ne a goshinsa kuma nan take suka tsere.

Ya bayyana cewa an ankarar da yan kungiyar sintiri a Gada-Biyu inda suka isa wajen da al'amarin ya faru amma sun isa a lokacin da tuni maharan su tsere.

Maharan sun je yankin ne kawai suka harbe matashin sannan suka yi gaba ba tare da daukar wani abu ko yin garkuwa da wani ba.

A cewar mazaunin unguwar, babban jami'in dan sanda a SP Tony Oblano tare da wasu yan sanda uku da wani shugaban Fulani a Kwali da wasu yan kungiyar sintiri sun ziyarci wajen da abin ya faru.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa kakakin rundunar yan sandan Abuja, ASP Maryam Yusuf ba ta dauki kiran wayar da aka yi mata ba sannan kuma bai amsa sakon wayar da aka aika masa ba.


-Rahoton BBC HAUSA

Post a Comment

0 Comments