'Yan Bindiga Sun Kona Gidan Gwamnan Imo, Sun Kashe Jami’an Tsaro


Jaridar Aminiya ta labarto cewa; ’Yan bindiga sun kai hari gidan Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma tare da harbe jami’an tsaro suka kuma kona gidan.

Maharan sun mamaye gidan gwamnan da ke mahaifarsa a garin Omuma ne da sanyin safiyar Asabar, suka kashe jami’an tsaro biyu da ke gadin gidan  da kafin su cinna masa wuta.

Kwamishinan Yada Labarai da Dabaru na Jihar, Declan Emelumba, ya shaida wa Aminiya cewa “Kimanin jami’an tsaro biyu da ke bakin aiki a gidan gwamnan sun mutu.

“Wani jami’in NSCDC na daga cikin jami’an tsaron da suka rasa rayukansu a yayin harin.”

Bidiyon da aka wallafa a shafin gwamnan na twitter ya nuna yadda bangarorin ke ci da wuta.

Majiyarmu ta ce ’yan bindigar ba su raga wa hatta motocin da ke harabar gidan ba, inda su ma suka babbanka musu wuta suka kone kurmus.

Mazauna garin Omuma, mahaifar Gwamnan a karamar hukumar Oru ta Gabas ta Jihar Imo sun shiga cikin tashin hankali bayan ’yan bindiga suka kai harin.

Majiyarmu a garin ta ce duk da cewa jami’an tsaron da ke tsaron sun yi ta maza wurin fatattakar maharan, amma an fi karfinsu har ta kai ga mutuwar biyu daga cikinsu.

A wani kaulin kuma ’yan bindigar sun kashe wasu jami’an tsaro biyu a mahadar Oguta zuwa Mgbidi, hanyar da ke zuwa mahaifar gwamnan kafin su karasa zuwa gidan gwamnan.

Majiyar a gidan gwamnatin Jihar ta ce jami’an kashe gobara suna ta kokarin hana wutar yaduwa zuwa wasu sassan ginin.

Wata majiyar kauye ta shaida wa wakilinmu cewa sojoji sun mamaye yankin yayin da rikici ya mamaye yanayin.

Post a Comment

0 Comments