‘Yan Bindiga Sun Kwace Kauyaku 50 A Jihar Neja, Inji Gwamna Abubakar

 

Daga Auwal Adam

Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja ya bayyana cewa akalla kauyaku 50 ne a kananan hukumomi biyar na jihar ta Neja suka fada hannun ‘yan bindiga.

Gwamnan ya ce wadannan kauyukan yanzu babu kowa sakamakon hare-haren ‘yan bindigar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a garin Minna a yayin da yake bude taron horaswa na kwana biyu wanda aka shiryawa Daraktocin kananan hukumomi da kuma jami’an karbar haraji.

An shirya taron ne domin bunkasa hanyoyin tara kudaden shiga daga kananan hukumomi na jihar Neja.

Hukumar lura da kananan hukumomi na jihar ne ya shirya taron domin fito da hanyoyin tara kudaden haraji domin bunkasa ci gaban jihar da magance matsalolin da ake fuskanta da ya hada na matsalar tsaro da kuma kwararar ‘yan gudun hijira.

Gwamnan ya ce; “a yanzu haka akwai ‘yan gudun hijira dubu uku da suke zaune a sansanin ‘yan gudun hijirar a Minna, baya ga wadanda muke da su a sauran kananan hukumomin. A ina zamu samu kudaden da zamu lura da su?” ya tambaya.

Ya ci gaba da cewa; “akwai bukatar mu rage kudaden da muke kashewa, mu hada hannu domin ganin yadda zamu magance matsalar ma’aikatan boge da kuma masu sace kudaden jihar”, ya lurantar.

Ya yi gargadin cewa; gwamnati ba za ta ji kyashin korar wadanda ba sa kawo wani ci gaba ga tsarinta ba.

Gwamna Bello ya ce taron ya zo ne a daidai lokacin da kasar da kuma sauran kasashe  ke fuskantar matsalar tattalin arziki sakamakon matsalar tsaro da kuma annobar korona ba.

 

Post a Comment

0 Comments