'Yan Bindiga Sun Sace Uwa Da 'Ya'yanta Bayan Barin Wuta A Zariya


Daga Muhammad Haruna, Zariya

Rahotanni daga wakilinmu na Zariya da safen nan ya tabbatar mana da cewa; bayan musayar wuta da aka yi a tsakanin 'yan bindiga da jami'an tsaro a lokacin da 'yan bindigar suka kai hari a Unguwar Lowcost dake hanyar Kofar Gayan a Zariya, 'yan bindigar sun yi nasarar tafiya da wata mata mata suna Mariya da 'ya'yanta da zuwa hada rahotan nan ba a tantance adadinsu ba. 

Babu tabbacin ko masu garkuwar sun sace wasu sun tafi da su bayan Mariya da 'ya'yanta, amma wata majiya ta tabbatar mana da cewa; jami'an tsaron sun yi nasarar cafke mutum biyu cikin 'yan bindigar da suka kawo hari a cikin daren na Lahadi a yayin artabun. 

Idan ba ku manta a daren jiya Lahadi MADOGARA ta labarto cewa; da misalin karfe 11:15pm (na daren jiya Lahadi) ba abin da aka rika ji sai karar harbe-harbe ta ko'ina a Unguwar Lowcost dake Zariya ta jihar Kaduna. 

Duk kokarin da muka yi ta jin bakin Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige, amma abin ya ci tura ya zuwa hada rahoton nan. 

Har ya zuwa da safiyar yau Litinin, hukumomin jihar Kaduna ba su ce uffan ba kan lamarin. 

Garin Zariya na daya daga cikin garuruwan jihar Kaduna da 'yan bindiga suka fara yi wa baranaza a kwanakin nan, domin ko a makon da ya gabata MADOGARA ta labarto yadda 'Yan bindiga suka addabi kauyukan Zariya. 

A rahoton MADOGARA ta labarto cewa; 
a 'yan kwanakin gabanin shigowar azumi da cikin watan Ramadana bayanai sun tabbatarwa da MADOGARA cewa; wadansu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun adddabi kauyukan Zakara, 'Yan Durma, Mangi, Siddi da sauran kauyukan dake kewaye da garin Zariya ta jihar Kaduna.  

Bayanan wanda muka samu daga ganau sun tabbatar mana da cewa 'yan bindigar na zuwa ne akan babura da muggan makamai inda suke awon gaba da mutane da dabbobinsu tare da yi wa rayuwarsu barazana. 

Al'umma da dama da suke zaune a Kauyukan sun shaida mana cewa suna cikin firgici da su da dukiyoyinsu, inda yanzu ba sa bacci da ido biyu. Tuni da dama suka yi kaura suka bar kauyukan suka dawo kwaryar Zariya. 

Bincikenmu ya nuna cewa kauyukan ba su samun wani dauki daga jami'an tsaro a yayin da 'yan bindigar ke farmakar kauyukan. 

Duk wani kokari da muka yi domin jin ta bakin hukumomin tsaro a garin na Zariya, lamarin ya ci tura ya zuwa hada rahoton nan.

Post a Comment

0 Comments