‘Yan IPOB Sun Yanka Fulani 19 Bayan Sun Yi Musu Tsirara A Jihar Anambra

 


Daga Auwal Adam

Membonin kungiyar masu rajin kafa kasar Biyafara, IPOB sun kashe Fulani makiyaya guda goma sha Tara a garin Igbariam dake karamar hukumar Oyi ta jihar Anambra. 

Majiyarmu ta Jaridar DAILY NIGERIAN ta labarto cewa; tsageran IPOB din sun dira ne ginin da Fulanin ke zaune ne da misalin karfe 2 na daren ranar Lahadi, inda suka kashe mata goma sha biyu da maza bakwai da kananan yara da ba a tantace adadinsu ba. 

Har wala yau bayanai sun tabbatar da cewa tsageran IPOB din sai da suka fito da Fulanin waje suka yi musu tsirara, suka kuma daure su sannan suka yanka su.  

Wakilin majiyarmu ya samu wadansu hotuna marasa kyan gani na yadda aka kashe Fulanin. 

A wannan hoton kunai ya ganin yadda babu wadansu sassan jikin mutum a gawarwakin bayan sun kashe su. Wani mazaunin garin wanda ya bukaci da a sakaya sunansa, ya shaidawa majiyarmu cewa wadannan ‘yan IPOB din sun yanka maza uku, suka yanke al’aurarsu, matan suka yanke nononsu da cire zuciyarsu suka tafi da su. 

Majiyar tamu ta ce har wala yau sun kashe shanu 25, tare da raunata 19 da kuma yanke guda biyar. 

 “yara biyu yanzu haka suna asibiti. ‘yan ta’addan har wala yau sun yanke kan wani jajiri dan wata tara. Wani abin bakin cikin shi ne dukkanin wadanda lamarin ya shafa, iyali daya ne”, ya tabbatar.

Ya zuwa hada rahoton na, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, Ikenga Tochikwu, bai amsa kiran majiyarmu. 


Post a Comment

0 Comments