‘Yansakai Sun Kashe Fulani 20 A Jihar Zamfara


Daga Muhammad Farouk

Akalla mutum 20 aka kashe a yayin da aka yi arangama tsakanin ‘Yansakai da Fulani a Dansadau dake karamar hukumar Maru a jihar Zamfara. 

Ganau sun shaida cewa kisan na ramuwar gayya ce bayan da aka kashe mutum uku a Ruwan Tofa tare da sace shanu da dama. 

A cewar majiyarmu ta Jaridar PUNCH, Mohammed Nuhu, wani mazaunin yankin ya shaida cewa wadansu ‘yan bindiga ne suka kai hari a garin Ruwan Tofa, inda suka kashe mutum uku, cikin harda memban ‘yansakai da aka haramta su, sannan suka yi awon gaba da shanu. 

Nuhu ya ce shanun da aka sace sai aka kai su kasuwar Dansadau, inda kuma aka yi kacibis da ‘Yansakai din a yayin da suka je kasuwar domin duba dabbobin da aka sace. Nuhu ya ce wannan dalilin ne ya sanya ‘Yansakai din suka afka da hari a kasuwar, inda suka kashe mutum 20 na ‘yan kasuwar a kauyen. 

“suna ganin wadansu daga cikin shanun, sai suka haukace, suka rika cewa sato su aka yi, kuma suna son su san wa ya kawo su zuwa kasuwar. Sai aka nuna musu wadansu Fulani guda uku wanda suka ce shanunsu ne, amma sai suka kashe su, suka kwashe shannun”, inji Nuhu. 

Wani mazaunin yankin mai suna Alhaji ya shaida cewa duk da kokarin da suka yi na kiran hukuma su zo su shiga tsakani, amma sai suka ki zuwa. “mun roki gwamnati da hukumomin tsaro da su kawo mana dauki domin su cece mu, amma har ya zuwa yanzu babu wani jami’in tsaro da ya zo yankinmu”, ya tabbatar. Post a Comment

0 Comments