YANZU-YANZU: Ƴan Bindiga Sun Sake Hallaka Daliban Jami’ar Greenfield A Kaduna


Ƴan bindiga da suka sace ɗaliban jami’ar Greenfield a Kaduna sun sake kashe dalibai biyu daga cikin ɗaliban da suka yi garkuwa da su.

Cikin sanarwar da kwamishinan al'amuran tsaro na cikin gida, Samuel Aruwan ya fitar ya ce an tsinci gawar ɗaliban ne a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce “Gwamnatin Malam Nasir El-Rufai tana bakin cikin wannan mummunar aiki da aka yi wa ɗaliban da ba su ji ba ba su gani ba da aka sace yayin da suke ci gaba da neman iliminsu don samun makoma mai kyau.”

A makon da ya gabata ƴan bindigar suka kashe uku daga cikin ɗaliban waɗanda ƴan bindiga suka sace a ranar Tatalar da ta gabata.

Post a Comment

0 Comments