YANZU-YANZU: Boko Haram Ta Kai Hari A Garin Mainok Ta Jihar Borno


Rahotannin dake shigowa MADOGARA a halin yanzu na nuni da cewa mayakan kungiyar Boko Haram ta kai hari a garin Mainok wanda ke kilomita 60 tsakaninsa da birnin Maiduguri a titin Maiduguri zuwa Damaturu. 

Garin Mainok shi ne Hedikwatar karamar Hukumar Kaga dake jihar Borno. 

Majiyarmu ta Jaridar PUNCH ta labarto cewa mayakan na Boko Haram na kona gidaje da fasa shaguna a garin. 

Harin na zuwa bayan mayakan Boko Haram din sun kai hari a garin Geidam, inda aka kashe Boko Haram din da dama. 

Cikakken bayani zai zo daga baya

Post a Comment

0 Comments