YANZU-YANZU: Boko Haram Ta Kwace Iko Da Geidam!


Gidan Rediyon Jamus na DW Hausa ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa; rahotannin da ke shigo mana da dumi-dumi sun nuna cewa mayakan Boko Haram sun karbe iko da garin Gaidam a jihar Yoben Nijeriya bayan wani hari da su ka kai tun ranar Juma’a da yamma. 

Wasu mutanen garin sun tabbatarwa da DW cewa  cewa tun a ranar Juma‘a mayakan suka shiga garin kuma suka kwana a ciki, inda suka rarraba wasu takardu da ke neman jama'a su hada kai da Daularsu.

Ya zuwa yanzu babu cikakken karin bayani.

Ga kwafin takardar da suka raba; 

Post a Comment

0 Comments