YANZU-YANZU: An Cinna Wuta Kan Babbar Kotun Tarayya Da Ke Ebonyi


Rahotanni daga jihar Ebonyi da ke kudu maso gabashin Nijeriya na cewa wasu 'yan bindiga sun cinna wuta kan babbar kotun Tarayya da ke Abakaliki, babban birnin jihar kamar yadda Bbc Hausa ta labarto. 

Ginin kotun yana kusa da babbar hanyar Enugu/Abakaliki, kusa da ofishin jam'iyyar PDP da ke jihar.

Kafofin watsa labaran Nijeriya sun ambato mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Loveth Odah tana tabbatar da kai harin.

Sun bayyana cewa maharan sun yi amfani da bama-baman da aka hada da fetur wajen kona kotun.

Rahotanni sun ce wutar da ta tashi ta shafi dakin karatu da dakin mai gadin kotun.

Sai dai ba a samu rahoton rasa rai ba.

Tuni dai masu aikin kashe gobara suka kashe wutar, a cewar wasu majiyoyi.

Wannan lamari na faruwa ne a yayin da yankin kudu maso gabashin Najeriya ke fama da hare-haren masu fafutukar ballewa daga kasar na kungiyar IPOB.

A kwanakin baya rundunar 'yan sandan kasar ta dora alhakin kai hari kan hedikwatarta da kuma gidan yari da ke Owerri, babban birnin jihar Imo.

Post a Comment

0 Comments