YANZU-YANZU: An Ga Watan Azumin Ramadan A Saudiyya


Hukumomi a ƙasar Saudiyya da maraicen nan sun sanar da ganin watan Ramadan a yau Litinin.

Hukumar Masallatai Biyu Masu Daraja na ƙasar wato Haramain Sharifain ce ta sanar da hakan a shafinta na Facebook.

Sanarwar na nufin a gobe Talata za a tashi da azumin Ramadana.

Tun da fari dai sai da shafin ya wallafa hoton wasu manyan malamai na ƙasar a yayin da suke duban watan gabanin Magariba.

Post a Comment

0 Comments