YANZU-YANZU: INEC Ta Tsayar Da Ranar Zaɓen 2023


Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta tsayar da ranar zaɓen 2023 a ƙasar.

Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin taron yini ɗaya na sauraren dokar laifukan Zabe ta 2021, wanda kwamitin Majalisar Dattawa kan INEC ya shirya, inji rahoton Bbc Hausa.

"Bisa dokar da aka kafa hukumar, zaɓen 2023 zai kasance ranar Asabar 18 ga watan Fabrairun 2023, wanda ya rage saura shekara ɗaya da wata Tara da mako biyu da kwana shida daga yau."

Shugaban Hukumar ya ce suna fatan tsara jadawalin zaɓen da zarar an kammala zaɓen gwamnan jihar Anambra wanda za a gudanar a ranar 6 ga Nuwamban 2021.

"Don yin yin hakan, ya kamata a samu tabbaci game da tsarin dokokin zaɓe don gudanar da zaɓen. Muna da yakinin cewa Majalisar Tarayya za ta yi abin da ya kamata cikin lokaci," in ji shugaban INEC.

Ya ce Hukumar ta matsu ta san tanadin doka da zai jagoranci gudanar da babban zaɓen na shekarar 2023.

Karin bayani na tafe..

Post a Comment

0 Comments