YANZU-YANZU: An Kashe Auwalun Daudawa Da Ya Yi Tuban MazuruGidan Rediyon DW Hausa ya labarto cewa; an kashe Auwalun Daudawa, dan bindigar da ya jagoranci garkuwa da daliban sakandaren Kankara da ke jihar Katsinan Najeriya, ya kuma tuba sannan ya sake komawa ruwa a wannan makon. 

Kwamishinan Tsaro da Lamurran Cikin Gida na jihar Zamfara  Abubakar Justice Dauran ya tabbatarwa  da DW hakan a wannan yammaci. Kwamishinan ya ce Auwalun Daudawa ya shaida masu cewa ya tafi bikin ‘yan uwansa amma abun takaici ashe daji ya koma kuma da zuwansa ya kore garken dabbobin wasu Fulani inda nan take suka bindige shi.

Post a Comment

1 Comments