YANZU-YANZU: Majalisar Dokokin Kaduna Ta Kori Shagali Da Ayyana Kujerarsa A Matsayin Wacce Ba Kowa

Aminu Abdullahi-Shagali


Daga Muhammad Farouk

Majalisar dokokin jihar Kaduna, ta ayyana kujerar tsohon Kakakin majalisar, Aminu Abdullahi-Shagali a matsayin wacce ba kowa.

Abdullahi-Shagali dan majalisa ce dake wakiltar karamar hukumar Sabon Gari, an tsige shi a mukamin Kakakin majalisar ne a cikin watan Agustan 2020 tare da ba shi umurnin ya bai wa majalisar hakuri.

Majalisar dokokin a zamanta na ranar Talata, ta bayyana cewa; tun daga lokacin har ya zuwa yau ya ki ya bai wa majalisar hakuri, kuma ba ya halartar ayyukan majalisar sama da kwana 120 kamar yadda doka ta tanada.

Majalisar dokin ta kori Abdullahi-Shagali ne daga majalisar bisa korafin da dan majalisa mai wakiltar Zariya da kewaye, Alhaji Ahmed Mohammed, ya gabatar gaban majalisar akan a ayyana kujerar Aminu Abdullahi Shagali a matsayin wacce ba kowa, wanda nan take majalisar ta amince.

Majalisar dokokin ta gudana ne a yau Talata a karkashin mataimakin Kakakin majalisar, Isaac Auta-Zankai, har wala yau sun kori ‘yan majalisu hudu da ayyana kujerarsu a matsayin ba kowa na tsawon shekara daya.

Wadanda aka kora sun hada da; Mukhtar Isa-Hazo, tsohon mataimakin Kakakin majalisar, kuma dan majalisa mai wakiltar Basawa, sai kuma Nuhu Goroh-Shadalafiya dan majalisa mai wakiltar Kagarko, da kuma Yusuf Liman-Dahiru, dan majalisa mai wakiltar Kakuri/Makera sai kuma Salisu Isa, dan majalisa mai wakiltar yankin Magajin Gari.

Majalisar dokokin ta ce ta kore su ne saboda suna haifar da matsala tare da gudanar da ayyukan da ke raba kan ‘yan majalisar jihar.

Idan za ku iya tunawa a ranar 11 ga watan Agustan 2021, majalisar dokokin ta kori ‘yan majalisa uku har na tsawon wata tara, a lokacin da aka nemi Abdullahi-Shagali shi kuma ya bada hakuri.

Post a Comment

0 Comments