YANZU-YANZU: MTN Sun Dawo Da Tsarin Sayan Datar Shiga Intanet


A daren Juma'a ne kamfanin layin wayar salula ta MTN ta sanar da cewa sakamakon gyare-gayre domin bunkasa tsarin sayan Datar shiga Intanet da suke son yi, sun dakatar da tsarin har zuwa safiyar ranar Lahadi. 

Da safiyar yau Lahadi MTN suka aika sakonni ga kwastomominsu cewa sun dawo da tsarin sayan Datar ta shiga Intanet yanzu mutum na iya saya ba tare da matsala ba. 

"Ya kwastoma, kokarin bunkasawa da zamu yi da ya shafi tsarin sayan Datar shiga Intanet ya kammalu. Yanzu za ka iya sayan datar a dukkanin tsare-tsarenmu. Mungode da ka za6i MTN", a cikin sakon. 

Post a Comment

0 Comments