YANZU-YANZU: NBC Ta Ci Tarar Gidan Talabijin Na Channels Naira Miliyan Biyar


Daga Muhammad Farouk

Biyo bayan tattaunawar da gidan Talabijin na Channels Television ya yi da Kakakin kungiyar dake fafutikar kafa kasar Biyafara, IPOB, Hukumar dake lura da gidajen Rediyo da Talabijin ta kasa, NBC ta ci tarar gidan Talabijin naira miliyan biyar bisa sabawa dokar watsa labari da NBC din ta zargi gidan Talabijin din da yi.

Gidan Talabijin din a ranar Lahadi ya tattauna da Kakakin IPOB, Emma Powerful bisa kashe Kwamandan kungiyar Ikonso da gamayyar Jami'an tsaron Nijeriya suka yi.

NBC ta ci tarar Channels TV ne a wata takarda da Mukaddashin Daraktan NBC din, Farfesa Armstrong Idachaba ya aikawa Babban Manajan Darakta na Channels din, inda NBC ta bayyanawa Channels cewa a shirinta gidan Talabijin din na karfe 7 na yammacin ranar Lahadi 25 ga Afrilun 2021, gidan Talabijin din ya bar shugaban IPOB yana kira ga ballewa daga Nijeriya ba tare da gidan Talabijin din ya tsawata masa ba, sabanin dokokin watsa labarai na kasar.

Har wala yau NBC ta zargi gidan Talabijin din da barin wanda suka gayyata da yin kalaman batanci da yada karya da bayanan marasa inganci akan rundunar sojin Nijeriya duk da haramta kungiyar ta IPOB din da Kotun kasa ta yi kamar yadda NBC din ta ce. 

Post a Comment

0 Comments