YANZU-YANZU: Shekau Ya Sheke Kwamandansa Ya Nada Sabo


Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya nada Abu Muhammad a matsayin sabon Amirul Jaish wato 'Kwamandan Yaki', ga bangaren da yake jagoranta bayan kashe tsohon Kwamandan na shi, wato Abu Fatimah.

Kafar watsa labarai ta PRNigeria ta tattaro cewa Shekau da kansa ne ya harbe Abu Fatimah a makon da ya gabata, bisa zargin sa da cin amanar mazhabar su.

Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa wasu Shekau din har wala yau ya kashe wasu manyan kwamandojinsa guda biyu . 

Majiyar ta kara da cewa "Bayan wani rikici na cikin gida, Shekau ya kashe Abu Fatima, wani Kwamandansa kuma Amirul Fi'ya, wanda da ne ga fitaccen dan kasuwar Bama, Alhaji Modu Katakauma". 

Post a Comment

0 Comments