YANZU-YANZU: Tsohon Ministan Buhari, Mahmud Tukur Ya Rasu A Abuja


Daga Muhammad Farouk

Rahotannin dake shigowa MADOGARA a halin yanzu na nuni da cewa; tsohon Ministan ma'aikatu da cinikayya, Dr Mahmud Tukur ya rasu. 

Majiyarmu ta Daily Trust ta labarto cewa; Dr Tukur ya rasu ne da safiyar yau Juma'a. 

Dr Mahmud Tukur shi ne shugaban Jami'ar BUK na farko, kuma tsohon Darakta ne a Cadbury Nigeria. 

Makusantan Marigayin sun tabbatarwa da majiyarmu rasuwar ta shi. 

Dr Tukur ya kasance makusanci ne ga shugaban kasa Muhammadu Buhari. 

Ya rasu ne sakamakon wata cuta da ba a bayyana ba, inda aka garzaya da shi zuwa wani asibiti a Abuja daga gidansa dake Kaduna a daren jiya. 

"za a dawo da gawarsa zuwa Yola domin yiasa jana'iza", majiyarmu ta tabbatar.

Post a Comment

0 Comments