YANZU-YANZU: ‘Yan Bindiga Sun Dira Jami’ar Greenfield A Kaduna Sun Yi Awon Gaba Da Dalibai

 Daga Muhammad Farouk

Wadansu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari Jami’ar Greenfield dake jihar Kaduna. 

Ita dai Jami’ar Greenfield jami’a ce mai zaman kanta wacce ba ta gwamnati ba, wacce ta fara aiki shekaru uku da suka gabata, kuma mazauninta na kan titin Kaduna zuwa Abuja. 

Majiyarmu ta Jarirdar DESERT HERALD ta labarto cewa; wanda ya assasa jami’ar ya tabbatar musu cewa; tabbas an kai hari Jami’ar, kuma ‘yan bindiga sun sace dalibai da dama. Wanda ya ce ya zuwa yanzu ba su tabbatar da adadin daliban da aka sace ba. Amma majiyar tamu ta ce ‘yan bindigar sun kashe ma’aikacin Jami’ar daya a yayin da suka kai harin. 

Harin dai na zuwa ne kasa da mako daya da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya jaddada cewa rayuwa ba ta kamaci ‘yan bindigar ba, inda ya ce a maimaikon a tattauna da su, kamata yi a yake su a kashe su. Zantukan da wadansu ke ganin bai kamata gwamnan na bayyana su saboda yana kara harzuka ‘yan bindigar ne suna kai wa wadanda ba su ji ba ba su kuma gani ba hare-hare. 

Wadansu na da ra’ayin cewa ko da kuwa gwamnan na da irin wannan ra’ayin bai kamata yana fadarsu hakan ba a bayyane tunda an kasa magance ‘yan bindigar, domin a cewarsu hakan zai kawai kara harzuka ‘yan bindigar ne su yi ta kai hare-hare ba ji ba gani kan raunanan mutane. 

Majiyarmu Ta Zayyano Sunyen Dalibai maza da ‘yan bindigar suka yi awon gaba da su: 

Abraham Akinje

Fortune Alhassan

Miracle John

Miracle Turman

Jesse Jakiri

Joseph Davies

Abdullahi Yusuf

John Yari

Micheal Samson Ladan

Abdulkareem Ibrahim

Kabir Hamisu

Lemuel Adamu

Isreal Antonio

Isreal Musa

Nelson David

Mariam Nalado

Abdulkadir Abubakar

‘YAN BINDIGAR SUN KAI HARI A BARAKALLAHU GRA, KADUNA

Hakazalika majiyarmu ta ce wadansu ‘yan bindigar su ma sun kai hari a daren ranar Talata a Barakallahu GRA dake Rigacikun a garin Kaduna. Sai dai ‘yan banga da tsoffin sojojin dake yankin sun yi nasarar dakile harin na su. 


Post a Comment

0 Comments