YANZU-YANZU: An 'Yanto Daliban Kaduna 5 Cikin 39, Inji Samuel Aruwan


Daga Wakilinmu

Daliban makarantar horas da noma da Gandun Daji ta Kaduna guda biyar cikin 39 sun samu 'yanci. Inda yanzu haka za a duba lafiyarsu a asibitin sojoji.  

Kwamishinan al'amuran tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan shi ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwar manema labarai da ya fitar da yammacin yau Litinin. 
 

Aruwan ya ce rundunar sojin Nijeriya ta sanar da gwamnatin Kaduna cewa mutum biyar daga cikin daliban da aka yi garkuwa da su na makarantar Kwalejin koyar da aikin noma da gandun daji ta Afaka dake jihar Kaduna sun samu 'yanci. 

Samuel Aruwan ya ce gwamnatin Kaduna za ta bayar da cikakken bayani kan lamarin. 

Post a Comment

0 Comments