YANZU-YANZU: 'Yar Sardauna Ta Rasu A Dubai Tana Da Shekara 75


Aishatu Ahmadu Bello, 'ya ta biyu ga Marigayi firimiyan Arewan Nijeriya kuma Sardaunan Sakkwato, ta rasu tana da shekara 75 kamar yadda MADOGARA ta labarto.  

Marigayiyar mata ce ga Marigayi Marafan Sokoto, Ahmad Danbaba.

Danta Hassan Danbaba ya tabbatarwa da majiyarmu Ta DAILY NIGERIAN labarin rasuwar na ta. Inda ya ce ta rasu ne a wani asibiti a Dubai bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya. 

Danbaba ya ce ana shirye-shiryen dawo da gawarta daga Dubai zuwa Sakkwato domin yi mata jana'iza yadda addinin Musulunci ya tanada. 

Shi dai mahaifinta, wanda yake shi ne Firimiyar Arewa na farko kuma na karshe daga 1954 zuwa 1966, an kashe shi ne a juyin mulkin da sojoji suka yi. 


Post a Comment

0 Comments