An cika shekara ɗaya da rasuwar shugaban ma'aikatan fadar shugaba Buhari, Malam Abba Kyari. Abba Kyari ya rasu ne a ranar 17 ga wa...
An cika shekara ɗaya da rasuwar shugaban ma'aikatan fadar shugaba Buhari, Malam Abba Kyari.
Abba Kyari ya rasu ne a ranar 17 ga watan Afrilun 2020 sakamakon rashin lafiya.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana marigayi Abba Kyari a matsayin babban amininsa na hakika kuma mai kishin kasa.
Buhari ya ce Abba Kyari amininsa ne tsawon shekaru 42 suna tare kafin daga baya ya zama shugaban ma'aikata a fadarsa.
Malam Abba Kyari ya rasu ne yana da shekara 67 a duniya bayan ya yi fama da cutar korona.
No comments