Yau Sakataren Amurka Zai Tattauna Da Shugaba Buhari


Sakataren kasar Amurka, Antony Blinken zai tattauna da shugaba Buhari a yau Talata 27 ga watan Afrilun 2021. Zaman zai gudana ne ta Intanet. 


Kakakin Sakataren Amurka Ned Prince ne ya tabbatar da hakan a sanarwar manema labarai da ya saki. Inda ya ce Sakataren Amurka din zai gana da shugaba Buhari da Ministan lura da Harkokin wajen Nijeriya Geoffrey Onyeama a wani tattaunawar aiki tsakaninsu. 

Sanarwar ta ce zaman zai tattauna ne akan karfafa alakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma tattauna batutun masu muhimmanci. 

Zaman na zuwa ne bayan kasar Amurka ta gargadi 'yan kasarta da ka da su sake su je Nijeriya saboda matsalar tsaron da Nijeriya ke fama da shi a jihohi da dama. 

Post a Comment

0 Comments