ZARGIN BATANCI GA SAHABBAI: Gwamnatin Bauchi Ta Dakatar Da Wani Malami Daga Yin Wa'azi


Daga Wakilinmu

Cikin wata kwafin takarda da Kwamishinan addinai na jihar Bauchi, Honorabul Ahmad Aliyu Jalam ya fitar ya bayyana cewa an dakatar da Malamin daga yin Wa'az, huduba da kuma Limanci a fadin jihar Bauchi.

Kwamishinan ya ce; "bisa yanayin yadda malamin yake gabatar da wa'azinsa yana batanci ga Sahabban Manzon Allah (SAWW) wanda hakan zai iya haifar da fitina tsakanin al'umma", inji shi.  

Shi dai Sheikh Abubakar Idris mai Asasu shi me jagoran makarantar Asasudeen dake garin Azare wanda yake da tarin magoya baya.

Yana gabatar wa'azi a Unguwar matsango dake Azare. Ya kasance yana koyi da salon wa'azi irin ma Sheikh Abduljabbar Kabara wanda suke da'awar cewa akwai hadisai na Bogi da kuma Sahabbai da ba su inganta ba wanda suka ruwaito hadisai na jabu cikin littafan Musulunci.

Salon wa'azin na sa ya sanya suka samu sabani da fahimta da malamai masu yawa yadda aka yi ta kai ruwa rana tsakanin Abduljabbar Kabara da wasu Malamai a jihar Kano kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Bayanai sun nuna cewa; shima Malam Abubakar Asasu ya yi ta kokarin yin Mukabala tare da wasu Malamai kan fahimtarsa kafin zuwa lokacin da Gwamnatin jihar Bauchi ta dauki wannan mataki a kansa.

Wakilinmu dake Azare ya yi kokarin tuntubar Malamin domin jin matsayarsa game da wannan matakin da aka dauka a kansa. Sai dai yq zuwa yanzu ba su sadu da shi ba, amma da zaran ya samu zarafin ganinsa zamu yi hira da shi domin jin ta bakinsa.

Post a Comment

0 Comments