Zauren Facebook Na 'Home Of Solace' Sun Dauki Nauyin Jinyar Mai Ciwon 'Cancer'


Zauren sada zumunta na Facebook wanda ya shahara sosai wajen tallafa ma mutane tare da kawo ci gaba akan al'amuran yau da kullum harma da hada aure duka a zauren, ya sake taimaka ma wani bawan Allah dake jihar Katsina wanda Allah ya jarabce shi da ciwon daji da aka fi sani da 'cancer' da kudin da zai samu allura na wasu lokaci kafin magani. 

Wannan marar lafiya hotonsa ya yi yawo sosai a kafar sada zumunta amma bai samu wani tallafi ba sai yanzu, daya daga cikin uwa a wannan zaure na 'Home of Solace' ce ta wallafa a shafinta na zauren inda ta bayyana cewar sun yi iya bakin kokarinsu a zauren.

"Wannan mara lafiya na Katakawa dake be karamar hukumar Kankara mun hada naira dubu hamsin zamu bashi an jima ko gobe, zai zo asibiti a Katsina idan yaje zan masa 'transfer' ta 'account' na dan uwansu tare da yin waya a tabbatar an bashi."
 
"Dubu hamsin ba zai isa komai a lallurar tasa ba amma zai rage masa radadi ko da magani ne ya sha har Allah ya kawo masa agaji."

"an ce ciwon nasa 'cancer' ce kuma ya fara taba zuciyarsa, ba a cire tsammani ga lamarin Ubangiji zamu ci gaba da masa addua'ar samun lafiya. 

Inda a karshe ta yi Addu'a Allah ya saka ma wadanda suka taimaka da addu'oi ga wannan bawan Allah da kuma dukiya.

Post a Comment

0 Comments