Sabbin alkaluman da ma’aikatar
lafiyar Indiya da ta fitar a yau Asabar, sun nuna cewar rayukan mutum fiye da
dubu hudu annobar Korona ta lakume, yayin da wasu akalla dubu 401 suka kamu da
cutar cikin kwana daya rak a kasar.
Karin mutanen dubu 4 da 187 da cutar
ta kashe, ya sanya jumilar adadin mutanen da suka rasa rayukansu a dalilin
annobar kaiwa dubu 238 da 270, yayin da jimillar wadanda suka kamu da ita ya
kai kusan miliyan 22.
Karo na farko ke nan da adadin ya
kai haka tun bayan barkewar annobar a kasar.
Sai dai kwararru sun yi gargadin
cewa akwai yiwuwar adadin mutanen da cutar ta Korona ta kashe da kuma wadanda
suka kamu da ita a kasar ta Indiya ya zarce na alkaluman da ake da su, gami da
bayyana fargabar har yanzu annobar da ta sake barkewa karo na biyu ba ta
kololuwa ba.
Tuni dai kwararrun Birtaniya suka
bayyana damuwa kan sabon nau’in cutar Koronar da ya bulla a India, wanda suka
ce yana da hatsari kamar yadda rahoton RFI ya tabbatar.
0 Comments