A Fadawa Gwamnan Bauchi Wannan Lamarin!


Yanzu na fito kasuwa, ina zuwa babban shatale-talen kasuwar Central, sai na ga tsakiyar titin da ke zuwa Fada, da gaban kasuwar Isyaka Jibrin, duk kamar an share.

Na tsaya na tambaya Me ya faru?

Aka ce ai wai ma'aikatan BASEPA ne suka zo suka tattara dukkanin kayayyakin 'yan kasuwa da suka fito da su don sayarwa.

Sun loda motocinsu da kadarorin kasuwanci na raunanan mutane kananan 'yan kasuwa masu neman abin da za su ci da iyalansu a irin wannan bakin hali da al'ummar Nijeriya ke ciki.

Ina tsaye ban tafi ba, sai ga motocin ma'aikatan Basefar sun dawo cike da motoci.

Zuwansu ke da wuya suka suka rika dibar kayan mutane a cikin amalanke da Wilbaro, wadanda sun fito da su daga cikin kasuwar Isyaka Jibrin ne za su tafi wurin da za su kasa don neman Halal dinsu.

Yanzu haka dimbin mutane suna Zazzau ne sun yi tagumi cikin rudewa da rashin sanin makomarsu.

Mai dan jarin da bai wuce dubu 50 ba, ya debi bashin kaya na dubu 50 ko 70, yanzu an zo an kwashe duk kayan da sunan wai kula da tsabtar gari.

Shekara nawa bayin Allah din nan suka shafe suna irin wannan cin kasuwa na dan takaitaccen lokacin da bai wuce mako daya zuwa biyu ba??

Me zai hana a dagawa raunanan Talakawa bayin Allah kafa su dan samu albarkacin watan rahama na Ramadan, su dan samu halal din da za su ci da iyalansu??

Ina kira ga gwamnan jihar Bauchi, idan ya san da wannan abu da ake wa talakawansa masu karamin karfi, to ya dakatar da hakan.

Idan bai sani ba, to lallai ya takawa shugaban kula da tsabtar Muhalli ta Basepa birki kan wannan abu.

Ba yadda za a yi a ba mutane Notice din kasa da awa 24 su bar wurin kasuwancinsu, alhali ba a samar musu wani wuri na daban ba!

Lallai yana da kyau gwamnatin jihar Bauchi ta guji musgunawa raunanan talakawa, musamman a irin wannan wata mai alfarma, wanda Allah ke kishi da tausayin bayinsa. Lallai addu'ar wanda aka cutar mai kaifi ce!

Ina kira ga shugaban Basepa, akalla tunda kun tashe su ba tare da samar musu madadi ba, to ku ba su kayayyakin su su nemi inda za su ci abinci su da iyalansu.

Tun farko ba bukatar ku tattara kayansu ku kai ofishin ku ku yi garkuwa da su. 

Ai kuna da ikon hana kasa kaya a wurin, don haka ba sai kun yi kwacen kayayyakin ba. Wauta ne babba idan mataki na daya zai magance abu, a tafi zuwa mataki na uku kai tsaye!!

Jihar Bauchi tana daga cikin tsirarin jihohi masu zaman lafiya yanzu a Nijeriya, musamman kuma a arewa. Don Allah a tausayawa raunana, ko Allah zai ci gaba da jin tausayin mu zaman lafiyar da muke da shi ya dore, don lallai sakamakon cutar da wadannan mutanen zai iya zama babbar jarabawa ga jihar Bauchi.

Lallai a ba kananan 'yan kasuwa kayayyakin su a yau din nan, kuma ba tare da biyan wata tara ba!

ADAMU MUHAMMAD
Marubuci ne, kuma 'Dan jarida,  Reporter na jaridar ALMIZAN da POINTER EXPRESS.

Post a Comment

0 Comments