A Kul Dinku, Ku Kula Da Kalamanku –Sakon DSS Ga Malamai


Hukumar tsaron farin kaya ta Nijeriya wato DSS ta bayyana cewa daga yanzu ba za ta kawar da kai daga wasu mutane da ke neman tayar da zaune tsaye a kasar ba.

DSS ta soki abin da ta kira wasu kalamai na marasa son zaman lafiya da ke barazana ga gwamnati da dorewar kasar kamar yadda gidan rediyon BBC ya labarto.

Ta bayyana haka ne a sanarwar da ta fitar ranar Lahadi.

"Abin da ya ja hankalinmu shi ne kalaman da ba su dace da kuma wasu ayyukan malaman addini da shugabannin siyasa da suka gabata wadanda ko dai suka yi kira a cire gwamnati da karfi ko mkuma suke so a yi tarzoma. Mu gano cewa sun yi hakan ne domin kawo rashin zaman lafiya," a cewar DSS.

Hukumar ta kara da cewa abin takaici ne mutanen da ake gani da kima suna yin irin wadannan kalamai domin biyan bukatun kashin kansu.

"Muna masu tuna musu cewa kodayake mulkin dimokradiyya ya bayar da 'yancin fadar albarkacin baki, amma ba ta bayar da damar yin kalamai na ganganci da ka iya shafar tsaron kasa ba," in ji hukumar ta DSS.


Post a Comment

0 Comments