Sabon Shugaban Sojin Na bankwana Da Tsohon shugaban Sojin Marigayi I. Attahiru Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sabon Babban hafsa...
![]() |
Sabon Shugaban Sojin Na bankwana Da Tsohon shugaban Sojin Marigayi I. Attahiru |
Shugaban
kasa Muhammadu Buhari ya nada sabon Babban hafsan Sojojojin kasa, domin maye
gurbin Marigayi Laftanal Janar Attahiru Ibrahim wanda Allah ya yi wa rasuwa a
makon jiya sanadiyyar hadarin jirgin sama.
An
haifi sabon shugaban rundunar sojan kasar Manjo Janar Faruku Yahaya a garin
Sifawa dake karamar hukumar Bodinga a jihar Sakkwato a ranar 5 ga watan Janairu
1966.
Ya
samu gurbin karatu a kwalejin horar da kananan hafsoshin Soja ta NDA a rana 27
ga watan Satumbar shekarar 1985, inda ya kuma kammala a watan Satumbar 1990.
Janar
Yahaya ya rike mukamai daban-daban da suka hada da, shugaban runduar dake gadin
shugaban kasa, Darakta a kwalejin horas da manyan hafsoshin soja dake Jaji.
Yahaya
ya rike Babban jami’in gudanar da ayukan Soja a Hedikwatar soja ta kasa, ya
zamo shugaban ma'aikata a wata runduna ta musaman "Operation Pulo
Shield".
Kana
ya zamo baban jami’in soja a ofishin ministan tsaro kafin kuma ya zamo babban
Kwamandar runduna ta hudu, da shugaban rundunar yaki da ta’addanci ta zaman
lafiya dole.
Ya
rike shugaban sashin samar da horo na rundunar sojan kasa, kuma ya zamo babban Sakataren
rundunar soja na kasa. Ya kuma jagoranci runduna ta daya a matsayin GOC. Kafin
tura shi Maiduguri inda ya zamo shugaban rundunar hadin kai har zuwa lokacin
wannan nadi.
No comments