Alaba Ya Kulla Yarjejeniyar Shekaru 5 Da Real Madrid

 


Kungiyar Real Madrid ta sanar da kulla yarjejeniya da dan wasan Bayern Munich mai tsaron baya David Aalaba dan asalin kasar Austria.

Cikin sanarwar da ta fitar a wannan Juma’a, Madrid ta ce Alaba ya sauya sheka zuwa gare ta ne kan yarjejeniyar haska mata tsawon shekaru 5, bayan karewar wa’adin yarjejeniyarsa da Munich a karshen kakar wasa ta bana.

Real Madrid za ta gabatar da Alaba ga magoya bayanta bayan kammala gasar cin kofin kasashen nahiyar Turai ta 2020 da za a fara cikin watan Yuni.

Alaba da ya shafe shekaru 13 tare da Bayern Munich kafin rabuwa da ita, ya taimaka mata wajen lashe kofunan gasar Zakarun Turai 2, da kuma kofunan gasar Bundesliga ta kasar Jamus 10.

Samun tabbacin kulla yarjejeniyar Alaba da Real Madrid na zuwa ne kwana guda bayan da mai horas da kungiyar Zinaden Zidane ya sanar da ajiye aikinsa, matakin da ya soma aiki nan take.

Post a Comment

0 Comments