Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta zargi gwamnatin Nijeriya da gazawa wajen daukar matakan kare rayuka da dukiyoyin...
Kungiyar
kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta zargi gwamnatin Nijeriya da
gazawa wajen daukar matakan kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasar, gazawar da Amnesty
ta ce tana karawa miyagu kwarin gwiwar ci gaba da tafka ta’asa san ransu.
Amnesty
International ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta fitar yayin bikin
cikar ta shekaru 60 da kafuwa.
Rfi
Hausa ta labarto cewa; a cewar Daraktan kungiyar ta kare hakkin dan Adam a Nijeriya
Ossai Ojigho, kasar ta dade da tarihin fuskantar matsalar kasa magance take
hakkin dan adam, kare rayukan da dukiyar ‘yan kasar, tauye ‘yancin fadin
albarkacin baki da kuma rashin shugabanci na gari tun shekarar 1967.
Amnesty
ta kara da cewar ci gaba da salwantar da rayukan jama’a ta hanyar yi musu kisan
gilla da kuma sakacin gwamnati wajen murkushe miyagun tare da hukunta su, na ci
gaba da zama barazana babba ga hakkin rayuwa a Nijeriya.
Kungiyar
ta kuma koka kan yadda ‘yancin bayyana korafi ko ra’ayi ke fuskantar koma baya
a kasar ta Nijeriya, sakamakon dakile damar mutane ta gudanar da zanga-zangar
nuna bacin rai kan lamurran dake damunsu.
Wannan
dai ba shi ne karo na farko da Amnesty International ke wallafa rahoton dake
caccakar gwamnatin Nijeriya ba domin jan hankalinta kan kura-kuran da take
tafkawa, yayin da su kuma hukumomin Nijeriyar ke maidawa kungiyar martanin kare
kansu daga zarge-zargen da take musu, gami da yin watsi da wasu rahotannin da
suke bayyanawa a matsayin marasa tushe.
No comments