Amurka Mayaudariya Ce, Inji Shugaban Koriya Ta Arewa

 


A yau Lahadi Koriya ta Arewa ta zargi shugaban Amurka Joe Biden da bin manufofin nuna kiyayya, tana mai watsi da abin da ta kira diflomasiyyar yaudara ta Amurka, inda ta yi gargadin mayar da martani a kan duk wani cin zali da za a yi mata.

A ranar Laraba da ta gabata Biden ya ce gwamnatinsa za ta magance barazanar shirin nukiliyar Koriya ta Arewa ta hanyar diflomasiyya da takatsantsan kamar yadda RFI ta labarto.

A ranar Juma’a fadar White House ta ce a shirye shugaba Biden yake don tattaunawa da Koriya ta Arewa a kan batun jingine shirin nukiliyarta, biyo bayan kammala nazarin manufofi, amma Pyongyang ta mayar da martani tana cewa, Biden ya tafka babban kuskure.


Post a Comment

0 Comments