Amurka Za Ta Koma Yarjejeniyar Nukiliyar Iran


Rahotanni sun nuna cewa; a ranar Asabar bangarorin da ke cikin yarjejeniyar nukiliyar Iran sun tashi daga zagaye na uku na taron da suke a wani mataki na maido da Amurka cikin yarjejeniyar, inda ita ma Rasha ta bayyana kwarin gwiwar cewar za  a cimma gaci nan da makonni uku masu zuwa.

Wata majiyarmu ta diflomasiyya daga manyan kasashen da ke cikin yarjejeniyar ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa ba a kai ga fahimtar juna ba game da muhimman batutuwa ba, amma babu abin da zai gagara.

Jagoran tawagar Iran a taron, kuma mataimakin ministan harkokin wajen kasar, Abbas Araghchi ya ce tattaunawar ta kai wani muhimmin mataki.

Yarjejeniyar nukiliyar Iran na cikin halin rai kwakwai-mutu-kwakwai tun bayan da tsohon  shugaban Amurka Donald Trump ya janye kasarsa daga cikinta a shekarar 2018.

Post a Comment

0 Comments