Ƴan Bindiga Sun Sace Mutum 40 A Yayin Sallar Tuhajjud A Katsina


Wasu rahotanni daga jihar Katsina sun bayyana cewa kimanin mutum arba'in wanda ya haɗa maza da mata ne wadansu ƴan bindiga su ka yi awon gaba da su a daidai lokacin da su ke sallar Tahajjud a wani Masallaci da ke yankin Kwata a ƙaramar hukumar Jibiya ta jihar Katsina.

Ɗaya daga cikin mazauna ƙaramar hukumar Jibiya, Alolo Babangida Jby Abubakar ne ya tabbatarwa da Jaridar Kakaki Hausa faruwar lamarin.

Jihar Katsina dai na daga cikin jihohin da su ke fuskantar matsalar ƴan fashin daji da kan garkuwa da mutane tare da sace ɗalibai domin neman kuɗin fansa.

Post a Comment

0 Comments