An Ga Wata A Jamhuriyyar Nijar, Laraba Za A Yi Sallah


BBC Hausa sun labarto cewa; Gwamnatin Nijar ta sanar da ganin watan Shawwal, wanda ya kawo karshen watan azumin Ramadan a ƙasar.

Firainistan ƙasar Ouhoumoudou Mahamadou ne ya tabbatar da ganin jaririn watan.

Kuma a cikin sanarwar da ya yi ga ƴan ƙasa ya ce an ga watan ne a cikin yankunan Nijar uku.

Wannan na zuwa bayan Nijjeriya, makwabciyar Nijar ta sanar da cewa ba a ga watan ba tare da ayyana Alhamis a matsayin ranar Sallah. 

Post a Comment

0 Comments