An Gano Gawar Mutum 81 Daga Waɗanda Jirgi Ya Kife Da Su A Jihar Kebbi

 


Bbc Hausa ta labarto cewa; gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya ce ya zuwa yanzu an gano gawar mutum 81 daga cikin waɗanda jirgin ruwa ya kife da su a ranar Laraba da ta gabata.

Jirgin ruwan ya kife ne a garin Warrah na Ƙaramar Hukumar Ngaski da ke jihar bayan ya taso daga Lokon Minna na Jihar Neja.

Bagudu ya bayyana haka ne a jiya Lahadi yayin da yake tarɓar Gwamnan Katsina Aminu Masari, wanda ya je yi masa ta'aziyya, kamar yadda kamfanijn labarai na NAN ya rawaito.

Gwamnan ya ƙara da cewa garin Warrah na kusa da Kogin Neja da kuma Dam na Kainji.

"Har yanzu ana amfani da yankin wajen yin safarar kayayyakin amfani kuma dalilin da ya sa ake yawan samun zirga-zirgar jiragen ruwa kenan," in ji Bagudu.

"Akwai jirgin da zai iya ɗaukar kayan da suka kai nauyin babbar mota uku, akai kuma wasu jiragen da suke zuwa ƙasar Mali daga can.


"Amma wannan jirgin yana ɗauke ne da mutum 170 kuma ya kife a Warrah, inda mutum 22 ne kawai suka tsira. Ya zuwa yanzu, an gano gawar mutum 81 sannan ana ci gaba da aikin ceton."

Post a Comment

0 Comments