Shugabar Hukumar Kasuwanci ta Duniya WTO ta nada sabbin mataimaka hudu biyu daga cikinsu mata, karon farko da aka samu irin wannan sauyi a tarihin hukumar.
Ngozi Okonjo-Iweala, wadda ta kasance mace ta farko daga Afirka da ta yi nasarar darewa kan mukamin shugabancin hukumar, ta nada Ba’amurka Angela Ellard da kuma Anabel González ‘yar kasar Costa Rica a matsaiyin mataimakanta.
Sauran mutanen biyu da aka nada a matsayin mataimakan shugaban hukumar ta WTO mai babbar cibiya a birnin Geneva su ne Jean-Marie Paugam daga Faransa sai kuma Xiangchen Zhang dan kasar Sin.
Okonjo-Iweala, ta ce wadannan nade-naden na tabbatar da cewa tana da son samar da daidaito tsakanin jinsi a shugabancin wannan hukuma.
0 Comments