An Nemi Fasto Mbaka Sama Ko Kasa An Rasa, Mabiya Na Zanga-zanga


Daga Muhammad Haruna

Rahotannin da ke shigowa a halin yanzu shi ne an nemi Fasto Mbaka ko sama ko kasa an rasa. Fasto Mbaka dai kwanan nan ya caccaki gwamnatin shugaba Buhari akan matsalar tsaron kasar, inda ya nemi shugaban ya yi murabus ko a sauke shi saboda gazawarsa. 

A halin yanzu tuni mabiya malamin addinin Kirista Rabaran Ejike Mbaka suka mamaye tituna a Jihar Enugu da ke kudu maso gabashin kasar inda suke zanga-zanga bisa zargin cewa an kama jagoran na su.

Mutanen sun yi zargin cewa jagoran na su ya ɓace ne 'yan kwanaki bayan ya nemi Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya sauka daga muƙaminsa saboda ƙaruwar matsalolin tsaro a ƙasar.

Masu zanga-zangar na kiraye-kiraye ga cocin Catholic Bishop of Enugu da ta bayyana musu inda ya shiga.

Makusantansa sun faɗa wa dandazon mabiyansa da suka taru a yau Laraba cewa ba su sake ganinsa ba tun bayan da ya faɗa musu cewa zai je wata ganawa da Bishop kwana biyu da suka wuce.


Post a Comment

0 Comments