An Tsinci Jariri A Karkashin Bishiya A Jihar Neja


Daga Shafiu Umar 

A ranar 6 ga watan Mayun 2021 ne aka tsinci jariri a karkashin Bishiyan Mangwaro a wata Unguwa da ake kira Takacame a cikin Garin Bangi dake karamar Hukumar Mariga ta jihar Neja. 

Ya zuwa hada rahoton nan jaririn yana gidan Sarkin Garin ana ci gaba da kula da lafiyarsa, kuma bayanai sun nuna yana na cikin koshin lafiya.

A daidai wannan lokacin da al'umma ke cikin wani hali ne na matsin rayuwa, a daidai lokacin ne kuma ake jefar da jariri a karkashin Bishiya.

Post a Comment

0 Comments