An Yi Ganawar Sirri Tsakanin Majalisar Dattijai Da Shugabannin Tsaro


Daga Muhammad Farouk

Shafin Majalisar Dattijan Nijeriya dake Twitter ya wallafa cewa ana ganawar sirri tsakanin shugabannin tsaron Nijeriya da na 'yan Majalisar Dattijai. 

Hafsoshin tsaron na amsa gayyatar 'yan majalisar ce domin bayyana musu halin da ake ciki game da taɓarɓarewar tsaro a faɗin ƙasar.

Babban Hafsan Tsaro, Manjo Janar Leo Irabor ne ya jagoranci hafsoshin tsaron zuwa majalisar, inda Shugaban Majalisa Ahmad Lawan ya karɓe su.

Sauran jamia'n da ke amsa gayyatar sun haɗa da da shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta NIA da kuma na 'yan sandan DSS.

Bayan Sanata Ahmad Lawan ya gode musu bisa ayyukan kare tsaron ƙasa a madadin majalisar sai suka shiga tattaunawar sirri da misalin ƙarfe 11:21 na safen yau. 

Ya zuwa hada rahoton nan babu cikakken bayani dangane da ganawar ta su. 

Post a Comment

0 Comments