An Yi Kira Ga Gwamna El-Rufai Da Ya Soke Hawan Sallah A Zazzau Saboda Matsalar TsaroDaga Muhammad Farouk

An yi kira ga gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai da ya soke hawan sallah da sauran shagulgulan sallah da aka shirya za a yi a masarautar Zazzau saboda matsalar tsaron da ke kara ta'azzara a fadin jihar. Wannan kiran ya fito ne daga bakin Malam Musa Gambo Yakana a yayin zantawarsa da Jaridar MADOGARA inda ya jadadda cewa a maimaikon a tara cunkoson jama'a domin hawan sallah kamata ya yi a kira taro domin a yi addu'a ga jihar baki daya domin samun zaman lafiya.

Malam Musa har wala yau ya ce duba da yadda matsalar tsaro a jihar yake kazanta, kullum ana kashe wadanda ba su ji ba ba su kuma gani ba, tare da garkuwa da dimbin al'umma wanda har yanzu daliban Jami'ar Greenfield na hannun masu garkuwa da jama'a kuma ma ciki harda jikan Sarkin Zazzau, Marigayi Shehu Idris bai kamata a ce an taru ana hawan sallah da sauran shagulgula ba ya kamata ne a ce an gudanar da addu'o'i tare da nuna alhini kan abubuwan da ke faruwa a jihar. 

Malam Musa har wala yau ya nemi Masarautar Zazzau a karkashin Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli da ta yi koyi da Masarautar Daura wajen dakatar da dukkanin hawan da za a yi a Masarautar ta Zazzau saboda kare lafiya da dukiyoyin al'umma tare da gudanar da addu'o'i ga jihar. Sannan masarautar ta soke dukkanin wani lamuran ziyarar sallah da ake kai wa Sarki domin amfani da lokacin wajen yiwa jihar da ma kasa baki daya addu'a. 

"Bai kamata a ce gwamnatin jihar da sauran masu ruwa da tsaki su nuna halin ko in kula ba wajen shirya hawan salla a bana. A maimaikon haka a gudanar da addu'o'i kawai domin yi wa jihar da kasa baki daya addu'a", ya lurantar. 

Malam Musa Yakana ya bada misalai da dama na yadda a wadansu kasashe shugabanni ke fasa ziyarar aiki domin jajantawa al'ummarsa bisa ibtila'in da ke aukuwa. Inda ya nemi da su yi koyi da irin wadannan shugabanni wajen damuwa da al'ummarsu ba wai su shirya buki ba. 

Post a Comment

0 Comments