An Yi Wa Dan Jarida Dukan Kawo Wuka Saboda Wani Rahoto


Daga Muhammad Farouk

Frederick Olatunde Odimayo, wani dan rahoto mai zaman kansa, kuma Edita A Grace FM, wani gidan rediyo mai zaman kansa a jihar Kogi, ya ci bugu bayan harin da wadansu mutum biyar suka kai masa a ranar 16 ga watan Afrilun 2021, sakamakon rahoton fallasa da ya wallafa kan safarar miyagun kwayoyi a jihar, Jaridar MADOGARA ta labarto.

A rahoton da kwamitin kare hakkin ‘yan jarida ta CPJ ta wallafa, an yi wa dan jarida Odimayo dukan kawo wuka ne har sai da ya daina numfashi.

Rahoton wanda ‘Wadata Media and AdvocacyCentre (WAMAC)’ ta wallafa a ranar 31 ga watan Maris, ta bayyana cewa Odimayo ya yi shigar burtu ne wajen samo rahoton a matsayin mai siyan kwayoyi.

Mutum biyar din da suka kai wad an jarida Odimayo hari da yamma a wani shagon gyaran mota, sun ce dan jaridar ya kawo wa sana’arsu cikas inda rahotonsa ya tarwatsa sana’ar safarar miyagun kwayoyi.

Tuni aka kwantar da Odimayo, inda ya ce har yanzu ba ya jin dadin jikinsa sakamakon mahangurba da suka yi masa.

 ‘Yan sanda sun tabbatar da cewa sun kaddamar da bincike dangane da lamarin, a yayin da Odimayo ke ci gaba da karbar magani a asibitin Lokoja, babban birnin jihar Kogi, domin ganin ya samu lafiya.

Wani rahoto da ‘Reporters Without Borders’ ta wallafa, ya nuna cewa Nijeriya na daya daga cikin kasashen Afrika ta yamma da ‘yan jarida ke fuskantar barazana. Kuma a kidayar World Press Freedom ya sanya Nijeriya a 120 da ‘yan jarida ke fuskantar matsi.

Post a Comment

0 Comments